Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-04 20:33:21    
Ya kamata a ci gaba da kara musanyar ra'ayi a fannin al'adu tsakanin kasar Sin da kasashe na Larabawa da na Afrika

cri

A ran 3 ga wata a nan birnin Beijing, wakilin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin kuma tsohon jakadan Sin a kasar Masar Wu Sike ya furta cewa, ya kamata, a ci gaba da kara musanyar ra'ayi a fannin al'adu tsakanin Sin da kasashen Larabawa da na Afrika.

Wu Sike ya kara da cewa, a madadin karfin wata kasa, al'adu na iya kara zumunci a tsakanin kasa da kasa. Ya kamata, kasar Sin ta kara sanin kasar Masar da sauran kasashe na Larabawa da Afrika kan yanayin kasar Sin. Inda ya ce,

"Ina nuna goyon baya ga kara musanyar ra'ayi tare da kasashe na Larabawa da na Afrika. Kamata ya yi, mu kara gabatar da al'adun gargajiya da al'adun zamani da zamantakewa da tsarin siyasarmu ga mutanen duniya."

Mr. Wu ya gabatar da cewa, kasar Sin ta kafa cibiyar al'adu da makarantun Confucius biyu a birnin Cairo. Haka kuma, Sin da Masar sun kira "makon al'adu" da "makon sinima" sau da yawa a tsakaninsu.(Lami)