Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-04 16:42:01    
An kammala aikin share fagen taro a karo na biyu na majalisar wakilan jama'a karo na 11

cri

A ranar 4 ga wata, a nan birnin Beijing, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr. Wu Bangguo ya bayyana cewa, za a yi taro a karo na 2 na majalisar wakilan jama'a a karo na  11 a ranar 5 ga watan Maris, kuma yanzu an riga an kammala aikin share fage na wannan taro.


Wu Bangguo ya fadi hakan ne, a gun taron share fage a karo na 2 na majalisar wakilan jama'a na 11 ta kasar. Kana kuma a gun jawabinsa, ya jaddada cewa, ya kamata wakilan majalisar wakilan jama'a su sauke nauyin da ke bisa wuyansu bisa kundin tsarin mulki da dokokin shari'a na kasar, su dora muhimmanci sosai a kan hakkin jama'ar, don kammala dukkan ayyukan taron kasar, ta hakan, za a iya yin taron cikin tsarin demokuradiyya da hadin kai kuma bisa hakikanin abubuwan, da tayar da himmar al'umomin kasar da su yi kokari wajen sa kaimi ga bunkasuwar zamantakewar al'umma da tattalin arziki da kyau kuma cikin sauri, da yin aiki wurjanjan don samun wadata a zamantakewar al'umma daga dukkan fannoni.


Bayan da aka kada kuri'a kan taron share fage, an zabi sakatare janar da tawagar shugabannin taro a karo na 2 na majalisar wakilan jama'a ta 11 ta kasar. Kuma an zartas da jadawalin taron. Tawagar shugabannin babban taron, yana kunshe da mutane 171, Wang Zhaoguo zai zama sakatare janar na taron.(Bako)