A ran 3 ga wata, a birnin Beijing, Mista Hong Hao, shugaban hukumar daidaita harkokin taron baje koli na duniya a shekarar 2010 a Shanghai ya bayyana cewa, kasar Sin tana yin kokarinta kuma tana fatan Amirka za ta shiga taron baje koli na duniya da za a yi a shekarar 2010 a birnin Shanghai.
Mista Hong Hao ya ce, sabo da dokar Amirka ta hana a yi amfani da kudi na kasar don shiga taron baje koli na duniya, gwamnatin Amirka ta ba da iko ga wata hukuma ta musamman don tattara kudi na shiga taron baje koli na duniya a shekarar 2010 a Shanghai. Bugu da kari, ya bayyana cewa, taron baje koli zai nuna maraba da samar da hidimomi ga Amirka idan ta tabbatar da shiga taron.
Dadin dadawa, Hong Hao ya ce, taron baje koli zai yi aikinsa cikin adalci ga duk wanda zai shiga taron. Sabo da matsalar kudi da ake fama da ita, taron zai gabatar da sharuda masu dacewa da halin da ake ciki, da yin iyakacin kokarinsa na samar da hidimomi. (Asabe)
|