Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-03 22:30:17    
Ya kamata majalisar CPPCC ta ba da shawara ga gwamnati domin tinkarar matsalar hada-hadar kudi

cri

Ran 3 ga wata, a gun taron shekara-shekara na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta Sin wato majalisar CPPCC, Mr. Jia Qinglin shugaban majalisar ya nuna cewa, a shekarar da muke ciki majaliasr CPPCC za ta yi tattauna kan batuttuwan da ke shafe fadada bukatun da ake da su a gida, da kara karfin neman bunkasuwa mai dorewa, da yin shawarwari na musamman domin ba da shawara ga gwamnati wajen tinakrar matsalar hada-hadar kudi.

Mr. Jia Qinglin ya ce, a cikin shekarar da ta gabata, an hadu da mawuyacin hali a fannin hada-hadar kudi da tattalin arziki a duniya, kuma kasar Sin tana fuskantar kalubale mafi girma tun daga karni na 21. Game da haka, bi da bi majaliasr CPPCC ta jagoranci kwamitocin musamman da abin ya shafa dan yin tarurrukan fadin albarkacin baki domin ba da shawarwari kan ayyukan raya tattalin arziki, kuma ta ba da ingantattun shawarwari ga Jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin Sin da su daidaita manufar raya tattalin arziki daga manyan fannoni. A cikin shekarar da ake ciki, majlisar CPPCC za ta cigaba da lura da matsalar hada-hadar kudi ta duniya, da kuma zura ido kan matakai na sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da gwamnati ke tafiyarwa, tare da yin nazari yadda za a iya tinkarar matsaloli da yin hasashen yadda tattain arziki zai kasance. [Musa Guo]