Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-03 17:33:47    
(Sabunta)An kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin

cri

A ranar 3 ga wata da yamma, a nan birnin Beijing, an kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin. Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao da Jia Qinglin da dai sauran shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sun halarci bikin kaddamar da taron.

A gun taron, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin Jia Qinglin ya bayar da rahoton aiki ga mambobinsa da suka fito daga kungiyoyin jam'iyyun siyasa da al'umomi daban daban kimanin 2100 ko fiye. Haka kuma, ya yaba wa nasarorin da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin ta samu a shekarar 2008, kuma ya bayyana cewa, dole ne majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin ta mayar da ra'ayin mutane gaban kome, kuma a dora muhimmaci kan moriyar mutane, da ba da shawarwari kan ra'ayoyin jama'a da manufofi wajen kawo moriyar jama'a da kara daukar hakikanin matakai wajen taimakawa mutane.

Game da rahoton aiki na shekarar 2009, Jia Qinglin ya bayyana cewa, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin ta mayar da aikin bunkasa tattalin arziki mai kyau kuma cikin sauri a gaban kome, haka kuma ta mayar da aikin kiyaye zamantakewar al'umma mai jituwa gaban kome, da gudanar da matakai wajen ba da shawara kan harkokin siyasa cikin tsanake, da dudduba cikin demokuradiyya da kara shiga cikin harkokin siyasa da ba da shawarwari wajen harkokin siyasa, don kara gina zamantakewar al'umma da gaggauta ciyar da zamantakewar al'umma ta zamani gaba da ba da gudummawarta cikin himma.

Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, wata muhimmiyar hukuma ce da jam'iyyun siyasa da dama na Sin suka hada kai tare kuma suka ba da shawara kan harkokin siyasa a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin. Babban nauyin da ke bisa wuyanta shi ne, a yi tattaunawa da ba da shawarwari game da manyan manufofin da suka shafi siyasa da tattalin arziki da zaman rayuwar mutane da dai dukkan fannoni, da bayar da ra'ayoyi da shawarwari ga majalisar

Wannan taro shi ne taro a karo na 2 na kwamitin duk kasa na 11 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, kuma za a shafe kwanaki 9 ana yinsa, mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin kimanin 2100 ko fiye, za su halarci wannan taro, kuma za su saurara da dudduba rahoton aiki na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin, da rahoton aiki wajen gabatar da shiri. Kana kuma sun saurara da tattaunawa kan rahoton aiki na gwamnati, da rahoton aiki na babbar kotun koli ta jama'ar Sin, da rahoton aiki kan hukumar koli mai bincike laifuffuka ta jama'ar Sin, kazalika kuma za su bayar da shawarwari kan manyan manufofi game da aikin yin gyare-gyare da raya kasa da batutuwa da suka fi jawon hankulan mutane. (Bako)