Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-03 15:49:47    
An kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin

cri

A ranar 3 ga wata na yamma, a nan birnin Beijing, an kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin. Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao da Jia Qinglin da dai sauran shugabannin jam'iyyar kwaminis ta Sin sun halarci bikin kaddamar da taron.

Wannan taro shi ne taro a karo na 2 na kwamitin duk kasa na 11 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, kuma za a shafe kwanaki 9 ana yinsa, mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin kimanin 2100 ko fiye, za su halarci wannan taro, kuma za su saurara da dudduba rahoton aiki na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin, da rahoton aiki wajen gabatar da shiri. Kana kuma sun saurara da tattaunawa kan rahoton aiki na gwamnati, da rahoton aiki na babbar kotun koli ta jama'ar Sin, da rahoton aiki kan hukumar koli mai bincike laifuffuka ta jama'ar Sin, kazalika kuma za su bayar da shawarwari kan manyan manufofi game da aikin yin gyare-gyare da raya kasa da batutuwa da suka fi jawon hankulan mutane.

Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, wata muhimmiyar hukuma ce da jam'iyyun siyasa da dama na Sin suka hada kai tare kuma suka ba da shawara kan harkokin siyasa a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin. Babban nauyin da ke bisa wuyanta shi ne, a yi tattaunawa da ba da shawarwari game da manyan manufofin da suka shafi siyasa da tattalin arziki da zaman rayuwar mutane da dai dukkan fannoni, da bayar da ra'ayoyi da shawarwari ga majalisar.(Bako)