Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-03 11:07:54    
Shirin ba da shawara na farko na taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin ya mai da hankali kan batun samun aikin yi

cri
Rukunin karbar shawara na taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin a mataki na biyu a karo na 11 ya ba da labari cewa, "shiri game da warware batun samun aikin yi yayin da Sin take fuskantar matsalar kudi" da jam'iyyar Zhi Gong ta gabata ya zama shiri na farko na wannan taro.

Wannan shiri ya yi nuni da cewa, matsalar kudi da kasashen duniya ke fuskanta ta kawo tasiri ne maras kyau ga Sin, kuma bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ta ragu, wadannan abubuwa sun haddasa sabane-sabane a tsakanin masu samar da aikin yi da masu neman aiki. Sabo da haka, warware batun samun aikin yi na dalibai da na manoma 'yan cin rani ya fi muhimmanci.

Gami da wannan batu, an ba da shawara cewa, ya kamata gwamnatin Sin ta tsara manufar bunkasa masana'antu ta dogon lokaci daga duk fannoni, da wasu manufofin ba da tallafi cikin gajeren lokaci, don kara samar da aikin yi ga dalibai da manoma 'yan cin rani. Ban da wannan kuma, an ba da shawarar samar da karin dokoki da ka'idoji a game da samun aikin yi.(Asabe)