Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-02 21:57:41    
Kasar Sin tana kokarin kiyaye da kuma bunkasa al'adun kabilar Tibet

cri

Ran 2 ga wata, gwamnatin kasar Sin ta bayar da takardar bayani ta "shekaru 50 tun daga aka farar yin gyare-gyare a Tibet", inda ta nuna cewa, gwamnatin kasar Sin ta dauki ingantattun matakai domin bunkasa harshen Tibet da kare da yada kayan tarihi da al'adun gargajiya na Tibet.

A cikin wannan takarda, an bayyana cewa, kuma ana gudanar da manufar bunkasa Sinnanci, wato harshen kabilar Han da harshen kabilar Tibet tare, kuma a mai da harshen kabilar Tibet a matsayi mafi muhimmanci. Tsawon lokacin watsa shirye-shirye na harshen kabilar Tibet ta hanyar rediyo ya kai kusan awoyi 18, kuma ana watsa shirye-shirye na harshen kabilar Tibet kan TV ba dare ba rana, yawan jaridu da mujalloli na harshen kabilar Tibet ya kai 24, ban da haka kuma yanzu kasashen duniya sun riga sun zartar da tsarin kwamfuta na harshen kabilar Tibet, wannan harshe na farko ne daga cikin harsunan kabilu masu rinjaye na kasar Sin.

Ban da haka kuma, kasar Sin tana kokarin kiyaye kayan al'adu na tarihi da yawa na kabilar Tibet. [Musa Guo]