Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-02 21:29:48    
Jaridar People's Daily ta bayar da sharhi don taya murnar budewar taro na biyu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na 11 ta jama'ar kasar Sin

cri

A ran 3 ga wata a nan birnin Beijing, za a bude taro na biyu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na 11 ta jama'ar kasar Sin. Jaridar People's Daily ta bayar da wani sharhi a ran 3 ga wata don taya babbar murna ga wannan taro da kuma nuna fatan alheri gare shi.

A cikin wannan sharhi, an ce, shekarar 2009 shekara ce ta cika shekaru 60 da kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin, kuma shekara ce ta cika shekaru 60 da kafa majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'a da shirya tsarin hada gwiwa tsakanin jam'iyyu daban daban da kuma ba da shawara kan harkokin siyasa a kasar. Sakamakon da aka samu a wadannan shekarun da suka wuce sun tabbatar da cewa, wannan tsarin da jam'iyyar kwaminis ta Sin ta tsara shi ne tsarin da ya dace da yanayin kasar Sin, kuma shi ne tsarin siyasa mai sigar musamman ta kasar Sin.

Bugu da kari, sharhi ya ce, shekarar 2009 muhimmiyar shekara ce ta tinkarar kalubalen Sin ciki da waje da ingiza bunkasuwar sha'ani na jam'iyyar da kuma na kasar. Kamata ya yi, majalisar ba da shawara ta jama'ar Sin ta nuna goyon baya ga manyan ayyukan jam'iyyar da kasar ta tattara karfin duk jama'ar Sin don ba da gudunmmawa wajen haye wahalhalu da kafa sabon shafi na sha'anin zaman gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin.(Lami)