A ran 2 ga wata, Mr Zhao Qizheng, kakakin taro a karo na biyu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin na 11 ya bayyana cewa, ya zuwa ran 2 ga wata da karfe 12 na tsakiyar rana, ofishin sakatariya ya samu shawara 265 da suke shafar tattalin arziki, kamar kara bukatun jama'a a cikin gida da inganta cinikayya a yankin iyakar kasar Sin da sauransu, sun fi jawo hankali.
A gun taron manema labaru dangane da taron da aka shirya a karo na farko a ran 2 ga wata, Mr Zhao ya gabatar da cewa, kwamitin tsakiya ya bayar da shirin kebe yuan biliyan dubu 4 a cikin shekaru 2 masu zuwa domin karawa tattalin arziki kaimi, kuma membobi da yawa sun bayyana ra'ayin cewa, abu mafi muhimmanci shi ne yin amfani da kudin yuan biliyan dubu 4 yadda ya kamata, kada a dinga maimaita wasu ayyuka sau da yawa, dole ne a yi amfani da kudin wajen kyautata zaman rayuwar jama'a.
Kuma Mr Zhao ya bayyana cewa, membobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa sun mai da hankali sosai kan raguwar cinikayya a iyakar kasar Sin, da yadda za a kara cinikayya a wannan yanki. Dadin dadawa, sun mai da hankali kan batun kara samar da guraban aikin yi da rage gibin dake tsakanin birane da kauyuka da sauransu.
Za a kaddamar da taro a karo na biyu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na 11 a ranar 3 ga wata da karfe 3 na yamma a babban dakin taron jama'a, kuma za a rufe taron ne a ranar 12 ga wata da safe, wanda zai dauki tsawon kwanaki 9 gaba daya.(Fatima)
|