Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-02 15:19:25    
Wakilai da mambobi na yankin musamman na Hongkong na shirya shirin tarurruka biyu na kasar cikin tsanake

cri
A jajibirin tarurrukan majalisu biyu na shekarar 2009 na kasar, wakilai na majalisar wakilan jama'a da mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na yankin musamman na Hongkong, sun rubuta bayanai kan ra'ayoyinsu, da sakamakon bincike da suka yi, da shawarwari da za su bayar. Haka kuma, yadda za a gaggauta hada kai tsakanin yankin musamman na Hongkong da babban yankin kasar Sin, da magance rikicin hada-hadar da ake fuskanta ta hanyar dogara ga mahaifanta na kasar Sin sun zama abubuwan da suka fi jawo hankulan mutane.

A ranar 1 ga wata, a gun taron manema labaru da aka yi a yankin Hongkong, wakilai 2 na majalisar wakilan jama'a da mambobi 7 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na yankin Hongkong sun bayyana cewa, suna fatan za su iya bayyana halin da ake ciki a yankin Hongkong da ra'ayoyin jama'a ga kasar Sin a lokacin tarurrukan majalisu biyu na kasar. Haka kuma, sun yi imani cewa, majalisun biyu na kasar za su iya karfafa zukatansu, su kara dogara ga kasar Sin, don magance tasirin da rikicin hada-hadar kudi ya kawo.

Mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na yankin musamman na Hongkong Yang Xiaohua ya gabatar da shiri guda 5 wajen inganta mu'amalar mutane da jigilar kayayyaki a yankin tekun Zhujiang Delta. Ya bayyana cewa, a halin yanzu da muke ciki watau rikicin hada-hadar kudi na duniya ke ci gaba da samun tabarbarewa, ya kamata yankin Hongkong ya sanya karfi wajen sa kaimi ga hadin gwiwa a fannin tattalin arziki tare da yankin tekun Zhujiang Delta da sa kaimi da kawo sauki ga sufurin kasa da na sama a wurin.

Mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na yankin Hong Tan Yaozong ya bayyana cewa, rikicin kudi ya yi babban tasiri ga yankin Hongkong, amma a karkashin goyon baya daga mahaifanta watau kasar Sin, jama'ar Hongkong za su iya kara karfafa zukatansu, sun yi imani cewa, tattalin arziki na Hongkong zai sami makoma mai haske.

Wakiliyar majalisar wakilan jama'a ta yankin Hongkong Cai Suyu za ta gabatar da shawarwari a jere kan batun kiyaye muhalli a gun tarurrukan majalisu biyu na kasar.(Bako)