A ran 2 ga wata da safe, wakilan rukunin farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da suke halarar taron na biyu na majlisar wakilan jama'ar kasar Sin a karo na 11 sun isa birnin Beijing.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, wandanan wakilai suna zuwa daga Henan lardin mafi girma wajen fitar da hatsi na kasar Sin, sun mai da hankali kan batun ingancin abinci. Wakilin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma sakantaren birnin Sanmenxia na lardin Henan Li Wenhui ta nuna cewa, tabbatar da ingancin abinci da karawa manoma da kudin shiga da suke samu, wannan shi ne babban tushe na bunkasuwar tattalin arziki na kasar Sin mai dorewa.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, sauran wakilan na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin za su isa birnin Beijing a ran 2 ga wata.(Abubakar)
|