Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-03-01 19:41:46    
'Yan jaridu fiye da dubu 3 za su tattara labaru kan muhimman taruruka 2 na shekara-shekara na kasar Sin

cri
Ran 1 ga wata, a lokacin da yake zantawa da manema labaru, Zhu Shouchen, mataimakin darektan cibiyar watsa labaru kan taruruka 2 na shekara-shekara na NPC da CPPCC na kasar Sin ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu 'yan jaridu fiye da dubu 3 sun yi rajistar tattara labaru a yayin wadannan muhimman taruruka 2 na kasar Sin.

Mr. Zhu ya kara da cewa, wannan adadi ya kusa yi daidai da na shekarar bara, ciki har da 'yan jaridu fiye da dari 8 daga waje, yayin da wasu 440 daga yankunan musamman na Hong Kong da Macao da kuma Taiwan.

Ban da wannan kuma, Mr. Zhu ya nuna cewa, yanzu kasar Sin na kara bude kofarta ga waje, an kara watsa labaru kan tarurukan 2 ba tare da boye kome ba, haka kuma, wakilai mahalarta tarurukan sun kara nuna karfin zuciya da budaddiyar zuciya. Shi ya sa aka yi imani da cewa, 'yan jaridu za su kara samun sauki wajen tattara labaru kan wadannan taruruka 2.(Tasallah)