Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-26 15:57:44    
Ana gudanar da aikin share fagen bikin baje-koli na duniya da za a yi a birnin Shanghai yadda ya kamata

cri
A gun taron manema labaru da kwamitin shirya bikin baje-koli na duniya da za a yi a birnin Shanghai a shekara ta 2010 ya yi a ran 26 ga wata a birnin Beijing, an ce, ana gudanar da aikin share fagen bikin baje-koli na duniya da za a yi a birnin Shanghai yadda ya kamata.

Mataimakiyar darekatan kwamitin aiwatar da bikin baje-koli na duniya Zhong Yanqun ta nuna cewa, ya zuwa ran 23 ga wata, da akwai kasashe da kungiyoyi guda 231 da suka tabbatar da shiga bikin baje-kolin. Ban da haka kuma, ana ci gaba da gina gine-ginen bikin baje-koli, kuma an samu nasara wajen yin kulle-kullen ayyukan adabi.

Zhong Yanqun ta nuna cewa, ya zuwa yanzu, babu wata kasa ko kungiya na duk kasashen da kungiyoyin da suka tabbatar da shiga bikin ta janye jikinta, yawancin kasashen da kungiyoyin sun nuna himma da kwazo wajen shiga bikin baje-koli na duniya da za a yi a birnin Shanghai.(Abubakar)