Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-25 10:51:59    
Jami'in jihar Tibet yana sa kyakkyawan fata kan ci gaban tattalin arziki a Tibet a bana

cri

A kwanakin baya, wani jami'in ma'aikata da abin ya shafa na jihar Tibet ya bayyana cewa, ana sa kyakkyawan fata kan ci gaban tattalin arziki a Tibet a bana. Kwatakwacin kudin shiga na ko wani manomi ko makiyayi a Tibet a bana zai karu fiye da kashi 13 cikin dari bisa makamantan lokaci na shekarar da ta gabata, kuma yawan kudin samar da kayayyaki na Tibet zai karu fiye da kashi 10 cikin dari.

A ran 24 ga wata, a birnin Lahsa, yayin da yake hira da manema labaru, mataimakin shugaban tawagar bincike Tibet ta hukumar yin kididdigar ta kasar Sin Wu Jianhua ya bayyana cewa, matsalar kudi ba ta kawo tasiri mai tsanani ba, ci gaban jihar Tibet ya danganta da jarin da gwamnatin tsakiya ta zuba. Ya bayyana cewa, har zuwa shekarar 2010, gwamnatin tsakiya za ta zuba jari kudin Sin yuan biliyan 77.8 wajen aiwatar da ayyuka 180 a Tibet.

An gabatar da cewa, a shekarar bana, Tibet za ta yi amfani da kudin Sin Yuan miliyan 50 wajen farfado da harkar yawon shakatawa da bunkasa ta, ta yadda za ta karbi masu yawon shakatawa miliyan 3 na gida da na waje a shekarar da muke ciki.(Asabe)