Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-23 15:53:05    
Al'ummar Tibet na yin rige-rigen sayayya domin shiryawa bikinsu na sabuwar shekara

cri
A albarkacin lokaci na karatowar sabuwar shekara ta al'ummar Tibet, an buga talla a ko ina a manyan kasuwannin sayayya na birnin Lhasa da ke jihar Tibet, jama'a da dama na rike da takardar sayayya ta moriyar jama'a da gwamnati ta bayar, kuma sun je sayayya domin shirya bikinsu na sabuwar shekara nasu.

Tun daga ranar 23 ga watan Janairu, jihar Tibet mai cin gashin kanta ta fara ba da takardar sayayya ta moriyar jama'a da darajar kowacensu ya kai kudin Sin Yuan 800 ga mutanen da suka ji dadin ababen hawa mai albashi kalilan da ma'aikata da suka yi ritaya da yawansu ya kai dubu 68. Wannan shi ne karo na farko da jihar Tibet ta bayar da takardar sayayya ga mutane masu albashi kalilan.

Haka kuma, manyan kasuwanni na birnin Lhasa sun bude hanyoyin musamman domin kara kawo sauki ga jama'a da suka yi sayayya ta takarda, haka kuma an kebe wuraren musamman domin sayar da madara da abincin musamman na jihar Tibet da naman sa da akuya da dai sauran kayayyakin masarufi, don biyan bukatun jama'a.(Bako)