Shekara ta 2009, shekara ce ta cika shekaru 50 da aka fara yin gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin. A halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin jihar Tibet yana bunkasuwa yadda ya kamata, mazauna jihar kuma suna jin dadin zamansu na yau da kullum.
A cikin shekaru 50 da suka gabata bayan da aka fara yin gyare-gyare ta hanyar dimokuradiyya a jihar Tibet, tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta jihar sun samu manyan sauye-sauye, tattalin arzikin jihar ya sami bunkasuwa cikin sauri, haka kuma, zaman rayuwar mazauna jihar ya sami kyautatuwa kwarai da gaske. A shekara ta 2007, yawan GDP da Tibet ta samu ya zarce kudin Sin Yuan biliyan 34, wanda ya ninka har sau 59 idan an kwatanta bisa na shekara ta 1959. A waje guda kuma, kaddamar da hanyar dogo da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ya sanya kuzari ga sha'anin yawon shakatawa na jihar, a halin da ake ciki yanzu, sha'anin yawon shakatawa ya kasance babban ginshiki wajen bunkasa jihar Tibet. Kazalika kuma, zuwa shekara ta 2007, matsakaicin kudin shiga da manoma da makiyaya a jihar Tibet suka samu ya kai Yuan 2788. Dadin dadawa kuma, sharadin aikin jiyya na jihar Tibet ya sami kyautatuwa kwarai da gaske.(Murtala)
|