Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-18 15:51:37    
Tawagogin 'yan jaridu na gida da na waje sun gani ainihin Tibet

cri
Bisa labarin da jaridar People's Daily ta bayar, an ce, da akwai 'yan jaridu da yawa na tawagogin 'yan jaridu na gida da na waje da suka ziyarci jihar Tibet sun bayyana cewa, sun ga babban ci gaba da aka samu a jihar.

Daga ran 10 zuwa 13 ga wata, gwamnatin Sin ta gayyaci kafofin watsa labaru na kasashen waje kamar kamfanin dillancin labaru na Reuters da sauransu da kafofin watsa labaru na Sin guda uku da su kafa tawagar 'yan jaridu don ziyartar Tibet. 'Yan jaridu da yawa sun bayyana cewa, a da, sun mai da hankali kan batutuwa na musamman dake gami da jihar Tibet, amma wannan ziyara ta shaida musu babban ci gaba da aka samu a Tibet a cikin shekaru 50 da suka gabata.

Kuma wasu manema labaru na waje sun ce, a kwanakin baya, wasu sun ba da labari cewa, halin da jihar Tibet ke ciki ya yi tsamari, an cafke mutane da yawa. Amma abin gaskiya shi ne jama'ar Tibet suna cikin kwanciyar hankali. Sun bayyana cewa, suna iya fahimtar dalinlin da ya sa gwamnatin Sin ta kara karfin tsaro bayan da hargitsin da aka tayar a ran 14 ga watan Maris na shekarar da ta wuce.(Asabe)