Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-17 14:39:28    
An samu nasara a kan shirin ayyukan kimiyya da fasaha na bikin baje-koli na duniya da za a yi a birnin Shanghai

cri
A ran 16 ga wata, a birnin Shanghai, manema labaru sun samu labaru daga taron shugabanni na shirin ayyukan kimiyya da fasaha na bikin baje-koli na duniya, inda aka bayyana cewa, ya zuwa yanzu, an samu nasara a kan shirin ayyukan kimiyya da fasaha na bikin baje-koli na duniya a birnin Shanghai da ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin da gwamnatin birnin Shanghai suka shirya.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, tun da aka tafa tafiyar da shirin cikin shekaru 4 da suka wuce, an gudanar da ayyukan kimiyya da fasaha guda 140 na bikin baje-koli na duniya a fanonnin shirya gine-gine da makamashi da muhalli da nune-nune da tsaro da sauransu, an riga an yi amfani da yawancin ayyukan na yankin bikin baje-koli.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, shirin ayyukan kimiyya da fasaha na bikin baje-koli zai ci gaba da sa kaimi ga bunkasuwar motoci masu yin amfani da sabbabin makamashi da samar da lantarki ta hanyar zafin rana. A sa'i daya, za a kara yin binciken ingancin abinci da bayar da gargadi game da bala'i.(Abubakar)