Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-06 18:34:17    
Ana tabbatar da sakamakon da taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ya haifar kamar yadda ya kamata

cri

Mr. Zhai Jun, mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin

A ran 6 ga wata, Mr. Zhai Jun, mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin ya gana da wakiliyarmu musamman game da ziyarar da shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai yi a kasashen Asiya da wasu Afirka duka 5, inda ya bayyana cewa, Mr. Hu Jintao zai yi wannan ziyara ne lokacin da ake cikin shekara ta karshe ta tabbatar da sakamakon da aka samu a yayin taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Yanzu, ana aiwatar da shirye-shiryen da aka tsara a gun wannan taron koli kamar yadda ya kamata, kuma an riga an samu sakamako mai kyau.

Mr. Zhai ya bayyana cewa, a gun taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, a madadin gwamnatin kasar Sin, Mr. Hu Jintao ya sanar da matakai da manufofi 8 na kara yin hadin gwiwa bisa hakikanin halin da ake ciki a tsakanin Sin da Afirka. A cikin shekaru 2 ko fiye bayan wannan taron koli, ana aiwatar da wadannan manufofi cikin hali mai yakini. Kasar Sin ta kuma samar da karin tallafin kudi ga kasashen Afirka. Kasar Sin tana kuma kokarin samar da karin rancen kudi ga kasashen Afirka. A waje daya kuma, an riga an gama aikin soke harajin kwastam ga kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen Afirka wadanda suke fama da talauci kuma suke da huldar diplomasiyya a tsakaninsu da kasar Sin. Haka kuma, masana'antun kasar Sin suna kafa unguwannin raya tattalin arziki da cinikayya a wasu kasashen Afirka bisa shirin da aka tsara. Bugu da kari kuma, ya zuwa karshen shekara ta 2008, yawan mutanen Afirka da suka samu horaswa a kasar Sin ya kai fiye da dubu 11. Sannan kuma, kasar Sin tana kara saurin gina cibiyoyin nuna misalin koyo na aikin gona da asibitoci da cibiyoyin shawo kan cutar zazzabin cizon sauro, wato Malaria da makarantu a kauyuka na Afirka bisa shirin da aka tsara. (Sanusi Chen)