![]( /mmsource/images/2009/02/06/hu.jpg) Lokacin da Zhai Jun, mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin ke zantawa da wakilinmu a ran 6 ga wata a birnin Beijing, ya bayyana cewa, shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai ziyarci kasashen Asiya da Afirka biyar daga ran 10 ga wata, wadda za ta kara inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashe masu tasowa, da kuma karfafa dankon zumunci tsakanin Sin da Afirka da kuma tsakanin Sin da Larabawa don kara samun bunkasuwa tare.
Kuma Zhai Jun ya ce, wannan shi ne karo na farko da shugaba Hu Jintao zai yi ziyara a shekara ta 2009. Kuma kasar Sin tana fatan ziyarar za ta iya karfafa dangantakar aminci tsakanin Sin da Saudi Arabia bisa manyan tsare-tsare, da inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da kwamitin hadin kan yankin gulf, da sa kaimi ga aiwatar da sakamako mai kyau na matakin karshe da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afirka, da kara ciyar da dangantakar abokantaka ta sabon salo tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare zuwa gaba, da kuma kara hadin gwiwar aminci tsakanin Sin da kasashen Afirka hudu, wato Mali da Senegal da Tanzania da kuma Mauritius.(Kande Gao)
|