A ran 4 ga wata, hukumar kula da harkokin bikin baje-kolin kasa da kasa ta birnin Shanghai ta kasar Sin ta bayyana wa 'yan jarida cewa, yanzu kungiyar EU da dukkan kasashe 27 membobin kungiyar sun tabbatar da shirin halartar bikin baje-kolin kasa da kasa na birnin Shanghai na shekarar 2010 a kasar Sin. Ya zuwa yanzu, kasashe 185 da kungiyoyin duniya 46 sun tabbatar da aniyarsu ta halartar bikin.
A cikin wasikar tabbatar da halartar bikin da kungiyar EU ta aika, kungiyar ta bayyana cewa, halartar bikin baje-kolin kasa da kasa na Shanghai ya karya tsohuwar doka ta EU kan rashin shiga bikin baje-kolin kasa da kasa a waje da kungiyar, wanda ya bayyana cewa, kungiyar EU ta dora muhimmanci kan dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Turai, kuma bangarorin ciniki da na al'adu na kasashen Turai sun dora muhimmanci kan kasar Sin da birnin Shanghai inda za a yi bikin baje-kolin kasa da kasa.
Za a fara bikin ne tun daga ran 1 ga watan Mayu zuwa ran 31 ga watan Oktoba na shekarar 2010, kuma babban taken bikin shi ne "birane na kara kyautata zaman rayuwar jama'a".(Zainab)
|