Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-03 17:38:48    
Shugaba Hu Jintao zai kai ziyarar aiki ga kasar Saudiyya da wasu kasashen Afirka

cri

Ran 3 ga wata, a gun taron manema labaru da aka yi a nan birnin Beijing, Madam Jiang Yu kakaki ta ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta sanar da cewa, bisa gayyatar da Sarki Abdullah Bin Abdul-Aziz na kasar Saudiyya, da shugaba Toumany Toure na kasar Mali, da shugaba Wade na kasar Senegal, da shugaba Jakaya Kikwete na kasar Tanzaniya, da shugaba Anerood Jugnauth da firaminista Ramgoolam na kasar Mauritius suka yi masa, Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin zai kai ziyarar aiki ga wadanan kasashe 5 tun daga ran 10 zuwa ran 17 ga wannan wata.

Madam Jiang Yu ta ce, shugaba Hu Jintao zai yi wannan ziyara ce domin karfafa huldar da ke tsakanin kasar Sin da wadannan kasashe, da shimfida sakamakon da aka samu a taron koli na dandalin hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da sa kaimi ga bunkasuwa tare. Yayin da shugaba Hu Jintao ke yin ziyara, shugaba Hu zai gana da shugabannin kasashen, za su yi musayar ra'ayoyi kan huldar abokantaka da ke tsakaninsu da harkokin duniya da yankunan da suka fi jawo hankulansu. [Musa Guo]