Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-13 20:28:51    
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya fara ziyarar aiki a kasashen Afirka 4 da kasashen Brazil da Portugal

cri
A gun taron manema labaru da aka shirya yau 13 ga wata a nan birnin Beijing, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Jiang Yu ta ce, daga yau ranar 13 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Mista Yang Jiechi ya fara ziyarar aiki a kasashen Afirka guda 4, ciki har da Uganda, da Rwanda, da Malawi, gami da Afirka ta Kudu, tare kuma da kasashen Latin Amurka guda 2, ciki har da Brazil, da Portugal.

Madam Jiang ta ce, ziyarar Yang Jiechi a kasashen Afirka 4 a wannan gami za ta taka muhimmiyar rawa wajen daukaka cigaban dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa tsakanin Sin da kasashen 4, da sa kaimi ga tabbatar da nasarorin da aka cimma a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka, tare kuma da ingiza sabuwar huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake kasancewa tsakanin Sin da Afirka.(Murtala)