A ran 29 ga wata, shugaban babbar kungiyar nuna jin-kai ta kasar Sin Mr. Fan Baojun ya bayyana a birnin Beijing cewa, bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, a cikin aikin yaki da bala'in girgizar kasa da aka yia jihar Sichuan da kuma ba da ceto a shekarar 2008, kungiyoyin nuna jin-kai na kasar Sin sun samu kudi da kayyayakin da aka bayar don yaki da bala'in da kuma ba da ceto da yawansu ya kai kusan kudin Sin Yuan biliyan 20.
Mr. Fan Baojun ya fadi haka ne lokacin da ya halarci bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ba da kudin taimako da aka shirya, inda aka ce, babbar kungiyar nuna jin-kai ta kasar Sin za ta ba da kudin taimako ga yankin shan wahalar bala'in girgizar kasa a jihar Sichuan don farfado da garinsu. Mr. Fan Baojun ya ce, a cikin aikin yaki da bala'in girgizar kasa a jihar Sichuan da kuma ba da ceto a shekarar 2008, kudin da kungiyoyin nuna jin-kai na duk kasa suka karba ya kai kashi daya cikin kashi uku na duk kudi da kasar Sin ta samu, wannan ya shaida cewa, kungiyoyin nuna jin-kai na kasar Sin suna da karfi sosai. (Zubairu)
|