Domin tabbatar da zaman rayuwar jama'a cikin lokacin hunturu yadda ya kamata a yankunan da girgizar kasa ta galabaitar da su, ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta kasar Sin ta yi kokarin fahimtar bukatunsu tare kuma da daukar dimbin matakai.
Matakan da ma'aikatar ta dauka sun hada da kira al'umma su ba da taimakon kayan sutura, don daidaita matsalar karancin sutura da ake fama da ita a yankunan da bala'in ya shafa. Sa'an nan, ta sa kaimi ga farfado da gidajen manoma da suka lalace sakamakon bala'in, kuma manoma wadanda ba su da gidajen kwana za su iya samun kudin taimako da yawansu ya kai yuan dubu 20. Ban da wannan, a ran 13 ga wata, ma'aikatar kula da harkokin jama'a tare kuma da ma'aikatar kudi ta kasar Sin sun ware kudaden da yawansu ya kai kudin Sin yuan biliyan 1 da miliyan 800 don taimaka wa jama'ar da ke yankunan da bala'in ya shafa.(Lubabatu)
|