Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-18 20:51:51    
Kasar Sin ta rigaya ta kasance tamkar injin bunkasa tattalin arziki sannan na'urar zaunar da shi da gindinsa a kasashen duniya

cri

A ran 18 ga wata a birnin Beijing, ministan kasuwanci na kasar Sin Chen Deming ya bayyana cewa, bayan da aka aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude koka ga kasashen waje a cikin shekaru 30 da suka wuce, kasar Sin ta rigaya ta kasance tamkar injin bunkasa tattalin arziki sannan na'urar zaunar da shi da gindinsa a kasashen duniya.

Bayan da Mr. Chen Deming ya halarci bikin nune-nune na tuna baya na cikon shekaru 30 da kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje da aka shirya a wannan rana, ya bayyana cewa, shekaru 30 da aka yi gyare-gyare a gida da bude koka ga kasashen waje, ya zama lokacin da kasar Sin ta samu bunkasuwa cikin sauri, yawan kudi na cinikayyar shige da fice na kasar Sin yana kara karuwa, ya ba da babbar gudumowa ga sha'anin cinikayyar duniya. A fannin zuba jari kuma, ko da yake kudin da kasar Sin ke zubawa a kasashen waje ya yi kadan a yanzu, amma yana karuwa cikin sauri a ko wace shekara, wannan kuma ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Mr. Chen Deming ya ce, a cikin matsalar kudi ta duniyar yanzu, sabo da sha'anin kudi na kasar Sin yana cikin halin tsanaki, sha'anin kera kayayyaki da na kashe kudi su ma haka. Wannan ya zaunar da tattalin arziki da gindinsa a kasashen duniya.

Bikin nune-nune na tuna baya na cikon shekaru 30 da kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje yana bisa jagorancin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin da sauran hukumomi da abin ya shafa, kuma an yi amfani da hotuna, da bayanai, da abubuwan tarihi, da kayayyaki, da fayil da yawa, don bayyana babbar nasara da kyakkyawan tarihi da kasar Sin ta samu wajen sha'anin bude kofa ga kasashen waje a cikin shekaru 30 da suka wuce. Daga ran 19 zuwa ran 30 ga wata, jama'a za su iya halarci bikin ba tare da biyan kudi ba. (Zubairu)