
A ran 18 ga wata, sabo da ya cika shekaru 30 da kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje, ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, da sauran hukumomin da abin ya shafa sun shirya bikin nune-nune mai hangen baya na cikon shekaru 30 da kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje a nan birnin Beijing.
A gun bikin an yi amfani da hotuna, da bayanai, da abubuwan tarihi, da kayayyaki, da fayil masu yawa, don bayyana babbar nasara da kyakkyawan tarihi da kasar Sin ta samu kan sha'anin bude kofa ga kasashen waje a cikin shekaru 30 da suka wuce. (Zubairu)
|