Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-18 20:44:28    
Gwamna Donald Tsang ya bayar da bayani don tunawa da cika shekaru 30 da aka aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude koka ga kasashen waje

cri
A ran 18 ga wata, gwamna Danald Tsang na yankin musamman na HongKong ya bayar da bayani mai taken "Shekaru 30 da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude koka ga kasashen waje, muhimmin gyara ne a zamani", don murnar cika shekaru 30 da kasar Sin ta aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude koka ga kasashen waje.

Mr. Donald Tsang ya bayyana cewa, a cikin shekaru 30, kasar Sin ta hadu da sauyi da bunkasuwa da yawa, wannan ya kawo tasiri mai zurfi ga yankin HongKong, a cikin shekarun nan, Hongkong ta shiga ayyukan yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin, kuma ta ba da babbar gudumowa. Yan kasuwar yankin Hongkong sun yi hadin gwiwa da kamfanonin babban yankin kasar Sin, wannan ya zama karo na farko ne da kasar Sin ta fara yin amfani da kudin waje. Ban da wannan kuma, akwai batun fasahar yadda za a kula da kamfanoni da yan kasuwar yankin Hongkong suka kawo ya na da muhimmanci sosai lokacin da babban yankin kasar Sin ya yi wa tsarin tattalin arziki gyare-gyare.

A cikin bayanin, Mr. Donald Tsang ya kara da cewa, yankin Hongkong zai yi amfani da damar ci gaba da yin gyare-gyare a gida da bude koka ga kasashen waje, da inganta hadin gwiwa da take yi da babban yankin kasar Sin, zai yi amfani da karfinsa, don kara ba da gudumowa ga bunkasuwar kasar Sin. (Zubairu)