Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-18 16:12:20    
Manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje wata muhimmiyar shawara ce da aka yanke

cri

Ran 18 ga wata a nan birnin Beijing, an kaddamar da bikin tunawa cika shekaru 30 da yin cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na 11 na jam'iyyar kwaminis ta Sin, a gun taron, Mr. Hu Jintao, babban sakatare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin sojojin kasar Sin ya jaddada cewa, manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa a waje wata muhimmiyar shawara ce da aka yanke wadda take jagorancin halin da ake ciki a zamanin yau.

Tun daga ran 18 zuwa ran 22 ga watan Disamba na shekarar 1978, an yi taro na uku na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin a karo na 11 a birnin Beijing. A cikin wannan taro, an yanke shawarar mai da ayyukan bunkasa tattalin arziki a matsayi mai muhimmanci, an fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje wadda ke da ma'anar tarihi.

Mr. Hu Jintao ya yabawa taro na uku na kwamitin tsakiya na J.K.S yana da muhimmin matsayi da ma'anar tarihi. Ya nuna cewa, yin gyare-gyare da bude kofa ita ce hanyar bunkasa Sin mai halayen musamman na gurguzu da farfadowar zaman a'ummar kasar Sin. Dole ne kasar Sin za ta cigaba da aiwatar da ayyukan yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, da sha'anin neman bunkasuwar zamani ta fannin gurguzu.