Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-14 21:55:42    
Bayan da Sin ta warware rikicin kudi da take fuskanta, tattalin arziki na wannan kasa zai hau wani sabon mataki

cri
A ranar 13 ga wata, firaminista na majalisar gudanarwa ta kasar Sin Wen Jia bao ya je gaida ma'aikatan ofishin jakadancin Sin da ke kasar Japan da Sinawa a Japan da hukumomin saka jari na Sin da ke kasar Japan da wakilan daliban Sin da ke kasar Japan kuma ya bayar da jawabi gare su.

A cikin jawabin da Mr. Wen ya yi, ya ce, yanzu, tattalin arzikin duniya ya yi tafiyar hawainiya, a sakamakon haka, yawan kayayyakin da Sin ke fitarwa a kasashen ketare ya ragu sosai, game da halin tattalin arziki mai tsanani da Sin ke fuskanta, kwamitin tsakiya na kasar Sin ya tsara wata muhimmiyar manufa watau ya kamata mu mayar da aikin ciyar da tattalin arziki gaba cikin kwanciyar hankali kuma cikin hanzari gaban kome, haka kuma ya kamata mu karkata hankulanmu wajen kara yawan bukatun sayayya a gida, musamman ma wajen kara yawan kudaden da mutane ke kashewa. Kwamitin tsakiya ya daidaita manufar tattalin arziki daga manyan fannoni cikin lokaci, kuma ya dauki matakan wajen kyautata manufofin kudi da tattalin arziki masu sassauci, kuma ya dauki wasu matakai a jere, don kyautata tattalin arziki daga manyan fannoni, kuma ya kamata mu hada ayyukan kara yawan bukatun sayayya a gida da ciyar da tattalin arziki gaba da raya zamantakewar al'umma da kyautata zaman rayuwar jama'a tare, yanzu ma'aikatun da abin ya shafa na gaggauta gudanar da ayyukansu daga manyan fannoni.(Bako)