Tun daga ran 8 zuwa ran 10 ga watan Disamba kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shirya wani taro a nan birnin Beijing, inda aka sanya aikin tabbatar da ci gaban tattalin arziki cikin hali mai dorewa kuma cikin sauri a kan matsayi mafi muhimmanci daga cikin ayyukan tattalin arziki da za a yi a shekara mai zuwa a kasar Sin.
A gun taron, Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya nazarci halin da ake ciki a nan kasar Sin da kuma duk duniya daga dukkan fannoni. Sannan ya bayar da muhimman ayyukan da ya kamata a yi a fannin tattalin arziki a shekara mai zuwa. A waje daya kuma, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya nazarci halin da ake ciki a fannin tattalin arzikin kasar Sin, kuma ya bayar da shirin raya tattalin arziki a shekara mai zuwa.
A gun taron, an nuna cewa, dole ne an sanya aikin habaka bukatu a kasuwannin gida ya zama wata tarbabiyar hanyar karuwar tattalin arziki. Sannan a sanya aikin canja hanyar raya tattalin arziki da kuma tsarin tattalin arziki ya zama muhimmin nauyin da ke bisa wuyanmu domin tabbatar da karuwar tattalin arziki. Bugu da kari kuma, za a kara karfin yin gyare-gyare a muhimman fannoni da batutuwa, kuma za a kara karfi wajen bude kofa ga kasashen waje domin tabbatar da karuwar tattalin arzikin kasar Sin. A waje daya, za a yi kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a, kuma wannan mafari da buri ne da ake son cimmawa lokacin da ake neman karuwar tattalin arziki.
Haka kuma, an bayyana cewa, muhimmin nauyin da ke bisa wuyan gwamnatin kasar Sin a fannin raya tattalin arziki a shekara mai zuwa su ne, kara da kuma kyautata aikin sa ido kan tattalin arziki daga dukkan fannoni. Kuma za a aiwatar da manufofin kasafin kudi da na kudi cikin hali mai yakini bisa halin da ake ciki. Haka kuma za a karfafa da kuma tabbatar da kyakkyawan halin da ake ciki a fannonin bunkasuwar aikin gona da kauyuka domin tabbatar da samar da isashen amfanin gona da karuwar kudin shiga da manoma ke samu da dai sauransu. (Sanusi Chen)
|