Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kammala ziyararsa a kasashen Amurka da Turai a cikin nasara, kuma ya dawo birnin Beijing a ran 27 ga wata.
A ran 14 ga wata, Hu Jintao ya fara kai ziyarar kasashen Amurka da Turai. A cikin ziyarar da ya yi, ya halarci taron koli na shugabannin kungiyar kasashe 20 kan tattalin arziki na duniya da kasuwanin duniya da aka shirya a kasar Amurka, kuma ya halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC a karo na 16 da aka shirya a birnin Lima babban birnin na kasar Peru, kuma ya yi ziyarar aiki a kasashe 4, wato Costa Rica da Cuba da Peru da Greece.
Hu Jintao da matarsa Liu Yongqing da sakataren sakatariya na kwamitin tsakiya na J.K.S kuma darektan ofishin kwamitin tsakiya na Sin Ling Jihua da sakataren sakatariya na kwamitin tsakiya na J.K.S kuma darektan ofishin binciken manufofin tsakiya na Sin Wang Huning da memban majalisar gudanarwa ta kasar Sin Dai Bingguo da 'yan rakiyarsu sun isa birnin Beijing tare.(Abubakar)
|