A ran 24 ga wata, Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya yi shawarwari tare da Karolos Papoulias, shugaban kasar Greece a birnin Athens. Bangarorin biyu sun bayyana cewa, za su inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni a tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi don amfana wa jama'ar kasashen biyu.
Hu Jintao ya nuna cewa, a cikin shekaru 36 da aka kafa dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Greece, an samu cigaba wajen dangantakar bangarorin biyu. Gwamnatin Greece da jama'arta sun nuna goyon baya ga wasannin Olympics na Beijing da na nakasassu. Gwamnatin Sin da jama'arta sun nuna godiya gare su.
Hu Jintao ya gabatar da shawara guda 4 wajen inganta dangantakar bangarorin biyu a tsakanin kasashen biyu. Na farko, za a zurfafa zumunci a tsakanin Sin da Greece, kuma za a kara amincewar juna a fannin siyasa. Na biyu, za a nemi sabon fanni don kara hadin gwiwa. Na uku, za a kara yin musanyar al'adu don zurfafa zumuncin jama'a. Na hudu, za a kara yin hadin gwiwa tsakanin bangarori da yawa don samu bunkasuwa tare.
Papoulias yana fatan bangarorin biyu za su kara yin hadin gwiwa a duk fannoni don inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu.
Hu Jintao ya yi bayyani kan halin taron koli a tsakanin kasashen G-20 game da kasuwar hada-hadar kudi da tattalin arzikin duniya da matakan da gwamnatin Sin ta dauka wajen habaka bukatu cikin gida da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki. Papoulias ya bayyana cewa, bangaren Greece ya darajanta gwamnatin Sin sosai da ta dauki matakai masu yakini don warware rikicin hada-hadar kudi na duniya.(Zainab)
|