Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-23 20:24:27    
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya ba da jawabi a gun kwarya-kwaryar taron koli a karo na 16 na APEC

cri

A ran 22 ga wata, a birnin Lima, babban birnin kasar Peru, an kaddamar da kwarya-kwaryar taron koli a karo na 16 na kungiyar hadin gwiwar kasashen Asiya da Pacific wajen tattalin arziki wato APEC, inda shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya halarci taro na matakin farko da aka shirya a ran nan da kuma ba da wani muhimmin jawabi.

Shugaba Hu ya bayyana cewa, karuwar tattalin arzikin duniya tana tinkarar matsalar kudi ta kasa da kasa. Ya kamata kasashe daban daban su dauki matakai cikin sauri domin hana yaduwar matsalar da kuma kwantar da kasuwar kudi ta duniya da kuma sa kaimi ga karuwar tattalin arziki. Haka kuma ya kamata kasashen duniya su yi kwaskwarima kan tsarin kudi na duniya bisa tushen yin shawarwari sosai tsakanin bangarorin da ke da nasaba da fa'ida. Kasar Sin tana son hadin kai tare da kasashen duniya wajen kiyaye kwanciyar hankalin kasuwar kudi ta duniya, haka kuma tana son yin kokari tare da membobin kungiyar APEC wajen inganta cudanya a tsakaninsu a fannin sha'anin kudi da kuma kara karfin kansu.(Kande Gao)