Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-22 16:54:51    
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya gana da shugaba mai daukaka na jam'iyyar KMT Lien Chan

cri

A ranar 21 ga wata a birnin Lima na kasar Peru, babban sakantare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin Mr. Hu Jintao, da matarsa madam Liu Yongqing sun gana da shugaba mai daukaka na jam'iyyar Kuomintang Mr. Lien Chan, da matarsa madam Lien Fang Yu.

A cikin ganawar, Mr. Hu Jintao ya nuna yabo sosai kan iyakacin kokarin da shugaba Lien ya yi kan bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan ta hanyar lumana a 'yan shekarun da suka wuce. Mr. Hu Jintao ya nuna cewa, yanzu dangantakar da ke tsakanin gabobin biyu na samun cigaba kamar yadda ya kamata. Kuma nasarar da saka samu wajen ziyarar da kwamitin kula da dangantakar tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan ya yi a kwanan baya ta nuna cewa, bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin gabobin biyu ta shiga wani sabon babi.

Bayan haka kuma, Mr. Hu Jintao ya jaddada cewa, kan matsalar kudi ta duniya da ake fuskanta a yanzu, ya kamata 'yan uwa na gabobin biyu su kara yin mu'ammala, da sa himma don ingiza hadin gwiwar tattalin arziki ta samun moriyar juna a tsakaninsu, don mayar da kalubale da ya zaman wata dama mai kyau.

Mr. Lien Chan ya yi farin ciki sosai da sake ganawa da Mr. Hu Jintao, yana ganin cewa, ganawar na nuna cewa, an kara yin hadin kai da samun bunkasuwa kan dangantakar da ke tsakanin gabobin biyu. (Bilkisu)