|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2008-11-17 21:55:53
|
Firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi bincike a yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa na lardin Sichuan
cri
Kwanan baya, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya kai ziyarar duba aiki a yankuna masu fama da bala'in girgizar kasa da ke birnin Mianyang na lardin Sichuan da ke yammacin kasar Sin, inda ya nuna gaisuwa ga mutane masu fama da bala'in a gidajen manoma, da masana'antu, da kuma marakantu, a waje daya kuma ya yi bincike kan ayyukan sake raya yankunan bayan bala'in.
Wannan ne karo na shida da Mr. Wen Jiabao ya kai ziyara a yankuna masu fama da bala'i bayan aukuwar babbar girgizar kasa a ranar 12 ga watan Mayu a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan. Mr. Wen Jiabao ya jaddada cewa, kara saurin ayyukan sake raya yankuna masu fama da bala'i, muhimmin mataki ne da aka dauka domin fadada bukatu na gida, da ciyar da bunkasuwar tattalin arziki gaba, shi ne kuma babban aiki na farko a gaban yankuna masu fama da bala'in. (Bilkisu)
|
|
|