Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-15 17:19:38    
Wenchuan tana daukar matakai domin ba da tabbacin zaman rayuwa a lokacin hunturu

cri
Yanzu a gundumar Wenchuan ta yankin kabilun Tibet da Qiang mai cin gashin kansa na lardin Sichuan, wato cibiyar mummunar girgizar kasa da ta auku a ran 12 ga watan Mayu, ana nan ana daukar matakai da dama cikin himma domin tabbatar da ganin dukkan mutane kimamin dubu 100 da girgizar kasar ta shafa sun sami ingantaccen tabbacin zaman rayuwa a lokacin hunturu.

Wakilinmu ya sami wannan labari ne a lokacin da yake neman labaru a wurin a kwanan baya. Zhang Yi, shugaban hukumar harkokin jama'a ta Wenchuan ya bayyana cewa, yanzu an tsugunar da dukkan fararen hula da girgizar kasar ta shafa a gidajen wucin gadi ko kuma gidajen da suka gina da kansu. Muhimmin aiki da ake gudanarwa a yanzu shi ne tabbatar da ganin fararen hula da girgizar kasar ta shafa sun sami isassun tufafin maganin sanyi da kuma abubuwan dumama daki da kuma abinci a lokacin hunturu.

Ban da wannan kuma, wannan jami'i ya kara da cewa, gundumar Wenchuan za ta gaggauta aiwatar da manufar kasar Sin kan bai wa mazauna kauyuka da girgizar kasar ta shafa kudin alawas da rancen kudi a fannin gina gidajensu da kansu, tana kokarin kammala gina gidajen din din din a kauyuka daga dukkan fannoni kafin karshen shekara mai zuwa.(Tasallah)