Ran 14 ga wata, bisa labarin da muka samu daga ma'aikatar harkokin jama'a ta kasar Sin, an ce, ya zuwa ran 10 ga wata, yawan kudin taimako da na darajan kayayyakin da kasar Sin ta karba daga bangarori daban daban na ciki da na waje ya kai RMB yuan biliyan 59.6, kuma an riga an samu yuan kusan biliyan 51 daga cikinsu, yawan kudin da kayayyaki masu daraja da aka samar ga wuraren da ke fama da bala'I ya kai fiye da yuan biliyan 27.3.
Madam Jiang Li mataimakiyar ministan harkokin jama'a ta ce, ma'aikatar harkokin jama'a ta riga ta kafa "tsarin kula da kudin taimako da kayayyakin taimako na ayyukan fama da bala'in girgizar kasa da ya faru a gundumar Wenchuan a ran 12 ga watan Mayu", ta haka domin kara sa ido kan yadda ake amfani da wadannan kudi da kayyayaki.
Bisa labarin da muka samu, an ce, ma'aikatar harkokin jama'a za ta kula da dukkan kudin taimako da aka samar domin fama da bala'in, za ta yi amfani da wadannan kudi yadda ya kamata.
|