Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-13 11:02:51    
Wu Bangguo ya isa kasar Seychelles ya fara yin ziyarar aiki ta sada zumunci a hukunce

cri

Bisa gayyatar James Alix Michel, shugaban kasar Seychelles da Patrick Herminie, shugaban majalisar dokoki ta kasar, Wu Bangguo, shugaban zaunanen kwamitin wakilan jama'a na kasar Sin ya isa Victoria, babban birnin kasar Seychelles a ran 12 ga wata da yamma, kuma ya fara yin ziyarar aiki ta sada zumunci ta kwanaki uku a hukunce a kasar Seychelles.

Da karfe uku da yamma a wannan rana, Wu Bangguo da tawagarsa sun isa filin jiragen sama na Victoria. Shugaba Michel da Mr Herminie sun isa filin jiragen sama don yin maraba da Wu Bangguo.

Wu Bangguo ya yi jawabi a filin jiragen sama, inda ya nuna fatan yin musanya ra'ayoyi tsakaninsa da shugaba Michel da Mr Herminie kan batutuwan da bangarorin biyu suka sa lura, kuma za su tattauta sabbin hanyoyi don kara hadin gwiwa da samun moriyar juna, ta haka za a kai zumuncin gargajiya tsakanin Sin da Seychelles zuwa wani sabon matsayi.(Zainab)