Bayan watanni shida da aukuwar mumunar girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichua na kasar Sin, an bude kofar wurin shan iska na tunawa da bala'in girgizar kasa na Dong Hekou da ke gundumar Qingchuan na lardin Sichuan a ran 12 ga wata, wanda ya zama wurin shan iska na farko na tunawa da girgizar kasa da ta auku a gundumar Wenchuan.
A wannan wurin shan iska, an nuna halayen kasa iri daban daban da ake ciki sakamakon aukuwar girgizar kasa. Haka kuma an rubuta lokacin aukuwar hadarin wato ran 12 ga watan Mayu na shekara ta 2008 da karfe 2 da minti 28 da yamma domin tunawa da tarihin aukuwar girgizar kasa.
A gun bikin bude kofar wurin shan iska, da farko mutane sun tsaya cik sun yi shiru har tsawon minti 1 domin nuna ta'aziyya ga mutanen da suka mutu a cikin hadarin. Kuma wani dan kauye ya bayyana cewa, hadarin girgizar kasa ya iya lalata gidajensu, amma bai iya lalata zukatansu ba, za su sake raya garinsu mafi kayatarwa.(Kande Gao)
|