A ran 11 ga wata, shugaban zaunannen kwamitin wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo dake yin ziyarar aiki ta sada zumunci a kasar Madagascar ya gana da shugaban kasar Marc Ravalomanana, firayim ministan kasar Charles Rabemananjara, shugaban majalisar dattijai ta kasar Yvan Randriasandratriniony da shugaban majalisar dokoki ta kasar Jacques Sylla.
A lokacin da ya gana da shugaba Ravalomanana, Mr. Wu Bangguo ya bayyana cewa, tun fil azal, ya kasance da zumanci a tsakanin kasashen Madagascar da Sin. A shekarun baya, sabo da kokarin aiki da bangarori biyu suka yi, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta samu babban ci gaba, kuma lokacin da ya fi kyau ga dangantakar tsakanin kasashen biyu ya yi. Bangaren Sin ya nuna godiya ga kasar Madagascar da ta tsaya kan manufar kasar Sin daya da ba da shawarwari masu kyau ga Sin a kan batutuwan Taiwan, Tibet, da na hakkin dan Adam. Shugaba Ravalomanana ya bayyana cewa, ayyukan hadin kai tsakanin kasashen biyu sun riga sun kai matsayin da ya kamata, kuma da akwai ayyuka da yawa da za a yi, musamman ma, bangarori biyu sun riga sun kafa dangantakar amince da juna a cikin tsawon lokacin da suka hada kai, wannan dangantaka za ta kawo moriyar juna a nan gaba.
A lokacin da ya gana da Mr. Rabemananjara, Mr. Wu Bangguo ya ce, dangantakar siyasa dake tsakanin kasashen biyu na da kyau, aikin zurfafa hadin gwiwa wajen tattalin arziki da cinikaya ya jawo hankalin kasashen biyu. Bangaren Sin yana son kara hadin gwiwa tare da bangaren Madagascar a fannonin makamashi, samar da ruwa da wutar lantarki, noma, horar da mutane da dai sauransu. Mr. Rabemananjara ya bayyana cewa, bangaren Madagascar yana son hadin kai da Sin sosai wajen karfafa ayyukan noma, makamashi mai bola jari, gina mayan ayyukan yau da kullum, kiwon lafiya, yawon shakatawa da dai sauransu, kuma yana nuna goyon baya kan hadin kai tsakanin kamfanonin kasashen biyu, da maraba da kamfanonin kasar Sin su kara shiga shirin ayyukan Madagascar.
A ran nan kuma, tare da shugaba Ravalomanana, Mr. Wu Bangguo ya halarci bikin daddale yarjejeniyoyin hadin kan tattalin arziki da cinikaya tsakanin gwamnatocin kasashen biyu, kamar yarjejeniyar hadin kan fasaha da tattalin arziki tsakanin gwamnatocin kasashen Sin da Madagascar. (Asabe)
|