 A ran 9 ga wata da safe, Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wanda ya kai wa kasar Habasha ziayarar sada zumunta a hukunce ya gana da Degefi Bula, shugaban majalisar dokoki ta kasar Habasha da Teshome Toga, shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar a babban ginin majalisar dokokin kasar.
Yayin da ya gana da Mr Degefi, Wu Bangguo ya bayyana cewa, kasar Habasha muhimmiyar kasa ce a nahiyar Afirka, kuma muhimmiyar kawa ce ta hadin gwiwa a tsakaninta da Sin a Afirka. Bangaren Sin ya dora muhimmanci a kan raya dangantakar tsakanin Sin da Habasha, kuma yana fatan kara hadin gwiwa tare da bangaren Habasha don ingiza dangantakar abokantaka daga duk fannoni a tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

Mr Degefi ya ce, dangantakar tsakanin kasashen biyu tana da kyau. Musanyar ra'ayoyin majalisar dokoki ta taka muhimmiyar rawa a fannin zurfafa zumincin jama'a da dai sauransu.
Yayin da ya ke shawarwari da Mr Teshome, Wu Bangguo ya jaddada cewa, kasar Sin da ta Habasha su kasashe masu tasowa ne, kuma suna da irin aikin raya kasa daya. Bangaren Sin yana son ci gaba da ganawa tsakanin shugabannin kasashen biyu, kuma su kara kyautata harkokin duniya da fadada fannonin hadin gwiwa da sa kaimi da nuna goyon baya ga masana'antun kasashen biyu da su hada kai don amfana wa jama'ar kasashen biyu.(Zainab)
|