Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-06 21:49:20    
Kasar Sin za ta halarci taron koli na kungiyar kasashe 20 bisa ra'ayi mai yakini

cri
A ranar 6 ga wata a nan birnin Beijing, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin He Yafei ya bayyana cewa, kasar Sin za ta halarci taron koli na shugabannin kungiyar kasashe 20 kan kasuwar kudi da tattalin arziki na duniya bisa ra'ayi mai yakini, kuma za ta yi kokari tare da bangarori daban daban da za su halarci taron, domin magance matsalar kudi ta duniya.

A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, Mr. He Yafei ya amsar tambayoyi kan ziyarar da shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai yi a tsakiyar wannan wata. A lokacin ziyarar, bisa gayyatar da aka yi masa, shugaba Hu Jintao zai halarci taron koli na kungiyar kasashe 20, da taron koli na shugabanni na kungiyar APEC, kuma zai kai ziyara ga kasashe hudu, ciki har da kasar Costa Rica.

Kan matsayin da kasar Sin ke tsayawa a kai a kan taron koli na kungiyar kasashe 20, Mr. He Yafei ya bayyana cewa, abin da ya cancanci a daidaita shi cikin gaggawa a gaban taron koli shi ne, daukar matakai masu amfani, don sake farfado da amincewa da kasuwa ta fannin jama'a, ta yadda za a hana tabarbarewar tattalin arziki a dukkan duniya, bugu da kari kuma, za a yi gyare-gyare a dukkan fannoni kan tsarin kudi na duniya bisa tushen yin shawarwari sosai a tsakanin bangarori daban daban, domin sa kaimi ga kafa tsarin tattalin arziki na duniya bisa tsari kuma cikin adalci. A waje daya kuma, ya jaddada cewa, ya kamata kasashen duniya su fi mayar da hankulansu kan tasirin da matsalar kudi ke kawowa kasashe masu tasowa. (Bilkisu)