Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-06 19:50:08    
Sin ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su inganta hadin-gwiwa don tinkarar matsalar hada-hadar kudi

cri

A wajen taron manema labaru da aka shirya ranar Alhamis din nan ne a birnin Beijing, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Qin Gang, ya bayyana cewar, ya kamata gamayyar kasa da kasa su inganta hadin-gwiwarsu, a wani kokarin tinkarar matsalar hada-hadar kudi kafada da kafada. Abun da ya kamata a ba fifiko shi ne, kasashe daban-daban su dauki kwararan matakai domin tabbatar da dorewar kasuwannin hada-hadar kudi.

Domin shawo kan matsalar hada-hadar kudi da ta dabaibaye duniya, asusun bada lamuni na duniya wato IMF ya bayyana fatansa na inganta hadin-gwiwa tare da kasar Sin. Yayin da Qin Gang ke amsa tambayoyin da manema labaru suka yi masa, ya ce, bangaren Sin yana ganin cewar, ya kamata a yi garambawul ga tsarin hada-hadar kudi na duniya, ta yadda wannan tsari zai kara taka rawarsa wajen sa ido kan harkoki, da sa kaimi ga hadin-gwiwar sassa daban-daban, domin tabbatar da habakar tattalin arzikin duniya mai dorewa. Qin ya cigaba da cewar, cimma wannan buri na bukatar bangarori masu ruwa da tsaki da su yi shawarwari ta hanyar dimokuradiyya kuma cikin daidaito, domin kafa wani tsarin hada-hadar kudi na duniya cikin adalci.(Murtala)