Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-06 10:48:21    
Wu Bangguo ya gana da firayim ministan kasar Algeria da shugaban majalisar dattijai wato kwamitin al'ummar kasar bi da bi

cri

A ran 5 ga wata, a birnin Algiers Shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo da ke ziyara a kasar Algeria, ya gana da firayim ministan kasar Algeria Ahmed Ouyahia da shugaban majalisar dAttijai wato kwamitin al'ummar kasar Abdelkader Bensalah bi da bi.

Lokacin da yake ganawa da Ahmed Ouyahia, Wu Bangguo ya ce, kasar Sin tana son kara hadin gwiwar samun moriyar juna tare da kasar Algeria bisa muhimman tsare-tsare cikin dogon lokaci, da nuna goyon baya ga kamfanonin kasashen biyu da su kara zurfafa hada gwiwarsu a fanonnin aiwatar da manyan ayyuka da kuma yin amfani da makamashi da albarkatu da kuma bunkasa yankin raya tattalin arziki da ciniki cikin hadin gwiwa da sauransu, da kara daga matsayin inganta hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da Algeria.

Ahmed Ouyahia ya ce, gwamnatin Algeria tana fatan kara saurin bunkasuwar dangantakar tattalin arziki da cinikaya tare da Sin, da kuma yin koyi da sakamakon da kasar Sin ta samu, da nuna goyon baya ga kamfanonin kasashen biyu da su kara hadin gwiwa a fanonnin gyara kayayyakin da gina gine-ginen manyan ayyuka da yin amfani da makamashi da haka ma'adinai da sauransu.

Lokacin da yake ganawa da Abdelkader Bensalah, Wu Bangguo ya ce, majalisar wakilan kasar Sin tana son kara sada zumanci da kwamitin al'ummar kasar Algeria da majalisar wakilan kasar a duk fanonni daban daban, da fara musayar sakamakon da suka samu a fannin kula da harkokin kasa da siyasa, da ba da sabuwar gudummawa ga kara zumanci tsakanin jama'ar kasashen biyu da bunkasuwar dangantakar tsakaninsu.

Abdelkader Bensalah ya ce, ziyarar da Wu Bangguo ya yi, ya sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar tsakanin kasashen biyu a duk gannoni, ko da yake ra'ayoyin jami'yyun da majalisar wakilai ba su sami ra'ayi iri daya ba, amma suna fatan kara hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.(Abubakar)