Yau a birnin Xi'an nan kasar Sin, an bude babban taron dandalin tattaunawa kan matsalar kudin duniya da kasuwannin kudin kasar Sin. Jami'an gwamnati da masanan ilmin tattalin arziki da 'yan kasuwannin hannayen jari sama da 600, ciki har da shugaban kwamitin kula da hannayen jari na kasar Sin, Mr.Zhou Daojiong, sun halarci taron, don tattauna hanyoyin da za a bi wajen tinkarar matsalar kudin duniya.
Za a shafe kwanaki biyu ana taron, kuma a lokacin taron, masana za su yi nazari a kan matsalar kudi ta duniya da makomarta da tasirinta da kuma halin da Sin ke ciki a fannonin tattalin arziki da kasuwanin kudi da kuma yadda za ta yi da dai sauransu, kuma za su ba da shawarwarinsu kan yadda tattalin arzikin kasar Sin da kasuwanin hannayen jari za su iya bunkasa yadda ya kamata.(Lubabatu)
|