Ranar 30 ga wata, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayar da wani rahoto cewa, tun daga shekaru 30 da suka wuce har zuwa yanzu, Sin ta aiwatar da tsarin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, manyan ayyuka da manyan gine-gine na kasar Sin sun sami ingantatuwa a bayyane, kuma sun kara taka rawa kamar wani babban ginshiki wajen bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma .
A cikin rahoton, an bayyana cewa, tun daga shekaru 30 da suka wuce, yawan jari da Sin ta zuba a kan manyan ayyuka da manyan gine-gine sun kara karuwa cikin hanzari, daga shekarar 1979 zuwa shekarar 2007, jimlar kudaden da Sin ta zuba wajen manyan ayyukan ta kai kimanin biliyan 30000, kuma ta kai kashi 38 cikin kashi 100 daga cikin dukkan jarin da Sin ta zuba wajen bunkasuwar zamantakewar al'umma. Kazalika kuma, an gudanar da manyan ayyuka kamarsu sufurin iskar gas daga yammacin kasar Sin zuwa gabashinta da tura ruwa daga kudu zuwa arewa, da mayar da gonaki don su zama gandun daji lami lafiya.
A cikin rahoton, an bayyana cewa, ta hanyar zuba jari a kan sha'anin manyan ayyuka, manyan ayyuka na Sin sun sami ingantatuwa sosai, kuma aikin gona da samar da makamashi dukkansu sun kai wani sabon matsayi, haka kuma hanyoyin zirga-zirga da sadarwa na kasar sun kasance tamkar wani gizo da zai iya game ko ina, haka kuma manyan ayyuka wajen kyautata muhallin ruwa da sha'anin ilmi da ala'adu da kiwon lafiya da motsa jiki su ma sun sami ingantatuwa a zahiri.(Bako)
|