A ran 29 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya aika da wani sakon nuna jejeto ga Alif Zardari, takwaransa na kasar Pakistan bisa mutuwar dimbin mutane da hasarar dukiyoyi da aka yi sakamakon babban bala'in girgizar kasa da ya auku a kasar.
A cikin sakonsa, Mr. Hu ya ce, bayan da ya samu labarin aukuwar bala'ini girgizar kasa a Pakistan, ya yi mamaki kuma ya ji takaici sosai sabo da mutuwar dimbin mutane da hasarar dukiyoyi da aka yi. Jama'ar kasar Sin wadanda suka yi fama da bala'in girgizar kasa na Wenchuan na lardin Sichuan sun san A wannan mawuyacin lokaci, a madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin baki daya suna nuna jejeto cikin sahihanci ga gwamnati da jama'a na kasar Pakistan, kuma na nuna ta'aziyya ga wadanda suka mutu a cikin bala'in.
A waje daya kuma, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya aika da sakon nuna jejeto ga takwaransa na kasar Pakistan. Mr. Yang Jiechi, ministan harkokin waje na kasar Sin ya kuma aika da wani sakon nuna jejeto ga takwaransa na kasar Pakistan. (Sanusi Chen)
|