Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-29 14:34:03    
Cinikayyar shigi da fici ta kasar Sin tana bunkasa lami lafiya

cri

A ran 28 ga wata, mataimakin ministan harkokin cinikayya na kasar Sin Mr. Gao Hucheng ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, yanzu, ana fuskantar da matsalar kudi na duniya, kuma cinikayyar duniya da tattalin arziki suna cikin hali mai tsanani sosai, amma cinikayyar shigi da fici ta kasar Sin tana bunkasa lami lafiya kuma cikin sauri, bunkasuwar cinikayyar shigi da fici na yanzu tana samun bunkasa mai kyau daga manyan fannoni.

Mr. Gao Hucheng ya bayyana cewa, tun daga shekarar bana, cinikayyar shigi da fici ta kasar Sin ta ci gaba da bunkasa lami kafiya kuma cikin sauri. A farkon watanni 9, kudin da aka samu daga cinikayyar shigi da fici ya kai kudin dalar Amurka sama da miliyan 190, ya karu sama da kashi 25 daga kashi dari idan a kwatanta da shi da na shekarar bara. Amma halin tattalin arzikin duniya ya kara tsanani, zai kawo babbar illa ga cinikayyar shigi da fici ta kasar Sin. A cikin farkon watanni 9 na shekarar bana, saurin karuwar cinikayyar fici dake tsakanin Sin da kasar Amurka, da kungiyar EU, da yankin Hongkong, da dai sauran yankuna ya ragu, saurin karuwar cinikayyar fici ta wadansu kayayyakin dake bukatar mutane da yawa shi ma ya ragu. Ban da wannan kuma, ra'ayin ba da kariya ga ciniki zai kara tsanani, halin da cinikayyar kasar Sin ke ciki kuma zai kara tsanani. (Zubairu)